Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Yaya za a iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum a washe kayansa, in ba an fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin ba? Sa'an nan ne za a iya washe gidansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 “Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:29
11 Iomraidhean Croise  

Kuna iya ku ƙwace wa sojoji wason da suka yi? Kuna iya kuɓutar da 'yan kurkuku daga ɗaurin masu baƙin mulki?


Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, Matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa Ya ɗauki rabon masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu.”


Ni kuwa in da ikon Ruhun Allah nake fitar da aljannu, ashe, Mulkin Allah ya zo muku ke nan.


Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.


Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa.


Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.


Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan