Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu a kan gāba, yă ɗore.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:25
18 Iomraidhean Croise  

Jama'ar Isra'ila suka rabu biyu. Rabi suka bi Tibni ɗan Ginat don su naɗa shi sarki. Rabin kuwa suka bi Omri.


Ka sa dukan abin da nake yi, Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.


Jama'ar Manassa da jama'ar Ifraimu suna fāɗa wa juna, tare kuma suke fāɗa wa Yahuza. Duk da haka fushin Ubangiji bai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.


Ni Ubangiji nakan bincike tunani, In gwada zuciya, Domin in sāka wa kowane mutum gwargwadon al'amuransa, Da kuma gwargwadon ayyukansa.


Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!


Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?


Nan da nan, da Yesu ya gane a ransa suna ta wuswasi haka a zuci, sai ya ce musu, “Don me kuke wuswasi haka a zuciyarku?


Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.


Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.


Amma in kuna cin naman juna, ku mai da hankali fa, hanyar hallaka juna ke nan.


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al'ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.


Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan