Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:18 - Littafi Mai Tsarki

18 “Ga barana wanda na zaɓa! Ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Zan sa masa Ruhuna, zai kuma sanar da al'ummai hanyar gaskiya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 “Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:18
40 Iomraidhean Croise  

Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce, “Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja, Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama'a.


Ikon Ubangiji zai ba shi hikima, Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa. Zai kuwa san nufin Ubangiji, ya kuma yi tsoronsa,


Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.


Ubangiji ya ce, “Bawana zai yi nasara a aikinsa, Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.


Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.


Ya Urushalima, al'ummai za su ganki mai gaskiya! Dukan sarakunansu za su ga darajarki. Za a kira ki da sabon suna, Sunan da Ubangiji ya bayar da kansa.


“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, ‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.’


Ka ji, ya Yoshuwa, babban firist, kai da abokanka da suke zaune gabanka, ku alama ce mai kyau. Ga shi, zan kawo bawana mai suna Reshe.


Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,


Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”


Aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai.”


Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.”


Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”


Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”


“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,


Sai aka ji wata murya daga cikin gajimaren, tana cewa, “Wannan shi ne Ɗana zaɓanɓɓena. Ku saurare shi!”


Domin wanda Allah ya aiko, zantuttukan Allah yake faɗa, gama Allah yana ba da Ruhu ba da iyakancewa ba.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”


Da suka iso, suka tara jama'ar Ikkilisiya suka ba da labarin dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa al'ummai ƙofar bangaskiya.


domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.


Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, tare da Timoti, ɗan'uwanmu,


Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,


Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah.


Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan