Amma sa'ad da bawana ya yi annabci, Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena, Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika. Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can, Za a kuma sāke gina biranen Yahuza. Waɗannan birane za su daina zama kufai.
Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”
Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa'an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.