Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. Sai suka tambayi Yesu, suka ce, “Ya halatta a warkar a ran Asabar?” Wannan kuwa don su samu su kai ƙararsa ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:10
21 Iomraidhean Croise  

Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha.


wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su.


Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.


“Taka ta ƙare, kai makiyayi marar amfani, Wanda yakan bar tumakin! Da ma takobi ya sari dantsensa da idonsa na dama! Da ma hannunsa ya shanye sarai, Idonsa na dama kuma ya makance!”


Amma da Farisiyawa suka ga haka, suka ce masa, “Ka ga! Almajiranka suna yin abin da bai halatta a yi ran Asabar ba.”


Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa su gwada shi, suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa a kan kowane dalili?”


Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.


suna haƙwansa su burma shi a cikin maganarsa.


Amma shugaban majami'a ya ji haushi, don Yesu ya warkar ran Asabar. Sai ya ce wa jama'a, “Akwai ranaku har shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo mana a ranakun nan a warkar da ku, ba ran Asabar ba.”


Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa babu?”


ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.


Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”


Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.”


A shirayin nan kuwa marasa lafiya da yawa sun saba kwanciya, makafi, da guragu, da shanyayyu. [Suna jira a motsa ruwan.


To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari'ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar?


Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa.


Saboda haka, waɗansu Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye Asabar.” Waɗansu kuwa suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai iya yin mu'ujizai haka?” Sai rabuwa ta shiga tsakaninsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan