Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:8 - Littafi Mai Tsarki

8 To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:8
11 Iomraidhean Croise  

Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.” Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”


A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.


A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa'ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama'a ba.


Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?


To, don me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa.


Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.


To, kallon me kuka je yi? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon gaske, masu zaman annashuwa, a fāda suke.


Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.


Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.


Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu,


Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan