Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:7
15 Iomraidhean Croise  

Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi.


To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.


Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba, Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, Har ya sa gaskiya ta ci nasara.


To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’


Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk ƙasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurinsa,


Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”


Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”


Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.


An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.


Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan