Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”
Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.
Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.
A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”
Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.
Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.
Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”
suka ɗaɗɗauko gazarin dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila!”