Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:29
38 Iomraidhean Croise  

Ubana ya tsananta muku ƙwarai, amma ni zan tsananta muku fiye da shi, ubana ya hore ku da bulala, amma ni zan hore ku da kunamai.’ ”


Kada ki yi shakka, ya zuciyata, Gama Ubangiji yana yi mini alheri.


'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai, Na bar yin fariya, Ba ruwana da manyan al'amura, Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina.


Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka.


Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi.


Matalauta da masu tawali'u za su sāke samun farin ciki wanda Allah Mai Tsarki na Isra'ila ya bayar.


Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’


Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.


(Musa dai mai tawali'u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.)


Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”


“Ku ce wa 'yar Sihiyona, Ga Sarkinki yana zuwa gare ki, Mai tawali'u ne, Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


“Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.


Sai jama'a suka firfito su ga abin da ya auku. Suka zo wurin Yesu, suka tarar da mutumin da aljannun suka rabu da shi, zaune gaban Yesu, saye da tufa, yana cikin hankalinsa. Sai suka tsorata.


Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku


In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.


Wannan shi ne Musan da ya ce wa Isra'ilawa, ‘Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin 'yan'uwanku, kamar yadda ya tashe ni.’


Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne.


Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,


Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.


Ku ɗauki halin Almasihu Yesu,


domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu.


yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.


da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya,


Kowa ya ce yana zaune a cikinsa, ya kamata shi kansa ma ya yi irin zaman da shi ya yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan