Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Ku zo gare ni dukanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:28
36 Iomraidhean Croise  

“Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.


Ai, an haifi mutum domin wahala ne, Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta suke tashi.


Kada ki yi shakka, ya zuciyata, Gama Ubangiji yana yi mini alheri.


Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji, Ƙarfina duka ya ƙare sarai, Kamar yadda laima yake bushewa, Saboda zafin bazara.


Ina nutsewa cikin ambaliyar zunubaina, Ina jin nauyinsu, sun danne ni ƙasa.


Don ka ba shi hutawa a kwanakin wahala, Kafin a haƙa wa mugaye kabari.


Na ga dukan abin da ake yi a duniya, duk aikin banza ne da ɓata lokaci kawai.


Kowane abu yana sa gajiya, Gajiyar kuwa ta fi gaban magana. Idanunmu ba sā ƙoshi da gani, Haka kuma kunnuwanmu ba sā ƙoshi da ji.


mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.


An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.


Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.


Ya miƙa muku hutawa da wartsakewa, amma kun ƙi saurarawa gare shi.


Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.


Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali'u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.


Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”


'Ya'yan Yonadab ɗan Rekab sun kiyaye umarnin da kakansu ya yi musu. Amma jama'an nan ba su yi mini biyayya ba.


Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’


Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.


Sukan ɗaura kaya masu nauyi, masu wuyar ɗauka, su jibga wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu ko tallafa musu da ɗan yatsa ba sa yi.


Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.


A ranar ƙarshe ta idin, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha.


Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?


Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”


Almasihu ya 'yanta mu, 'yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.


yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,


Saboda haka tun alkawarin shiga inuwarsa tana nan, sai mu yi tsananin kula, kada ya zamana waninku ya kāsa shiga.


Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan