Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Kowane abu Ubana ne ya mallakar mini. Ba kuwa wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban sai Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana wa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 “Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:27
21 Iomraidhean Croise  

Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.


Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”


Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.


kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.


Yesu kuwa, da yake ya san Uba ya sa kome a hannunsa, ya kuma sani daga wurin Allah ya fito, wurin Allah kuma zai koma,


“Na bayyana sunanka ga mutanen da ka ba ni daga cikin duniya. Dā ma naka ne, ka kuwa ba ni su, sun kuma kiyaye maganarka.


Uban yana ƙaunar Ɗan, ya kuma sa kome a hannunsa.


Ba wai don wani ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda yake daga wurin Allah, shi ne ya ga Uban.


Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.”


wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala'iku da manyan mala'iku da masu iko suna binsa.


Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan.


Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan