Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:25 - Littafi Mai Tsarki

25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:25
40 Iomraidhean Croise  

Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, “Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka.


Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa,


Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.


Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.


Saboda haka mutane suke tsoronsa, Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”


Yara da jarirai suna raira shi, Ka gina kagara saboda magabtanka, Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.


Kun shiga uku! A tsammaninku ku masu hikima ne, masu wayo ƙwarai.


Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?


A gare ka nake ba da godiya da yabo, ya Allah na kakannina, Gama ka ba ni hikima da iko, Har ka sanar mini da abin da muka roƙe ka, Ka sanar mana da matsalar da ta dami sarki.”


Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.


Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, “ ‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”


Ya ce, “Ya Uba, in dai ka yarda, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi”


Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.


Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.


“Yanzu ina jin nauyi a raina. Me zan ce kuwa? In ce, ‘Ya Uba ka ɗauke mini wannan lokaci’? A'a, ai, dā ma na zo ne takanas domin wannan lokaci.


Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi,”


Allahn da ya halicci duniya da dukkan abin da yake cikinta, shi da yake Ubangijin sama da ƙasa, ba ya zama a haikalin ginin mutum.


mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah.


Amma hankalinsu ya dushe, domin har ya zuwa yau, in ana karatun Tsohon Alkawari, mayafin nan har yanzu ba a yaye yake ba, domin ba ya yayuwa sai ta wurin Almasihu kaɗai.


Yaron nan Sama'ila yana ta aiki gaban Ubangiji, yana sāye da falmaran.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan