Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:22
22 Iomraidhean Croise  

ya aika da magana zuwa ga Sarkin Edom, da Sarkin Mowab, da Sarkin Ammon, da Sarkin Taya, da Sarkin Sidon ta hannun manzannin da suka zo Urushalima wurin Zadakiya Sarkin Yahuza.


“Ɗan mutum, Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya sa sojojinsa su matsa wa Taya. Kowane kai ya koɗe, kowace kafaɗa kuma ta yi kanta, amma duk da haka shi, tare da sojojinsa, bai sami hakkin wahalar da ya sha a Taya ba.”


“Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.


Hakika, ina gaya muku, a Ranar Shari'a za a fi haƙurce wa ƙasar Saduma da ta Gwamrata a kan garin nan.”


“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.


Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Saduma a kanki.”


Ina dai gaya muku, a Ranar Shari'a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi.


Amma a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,


Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da suke a nan a yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har ya zuwa ranar nan da za a yi wa marasa bin Allah shari'a, a hallaka su.


Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari'a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan.


Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.


Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan