Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al'ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:20
17 Iomraidhean Croise  

Na kula sosai, na saurara, Amma ba wanda ya faɗi wata maganar kirki, Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa, Kowa cewa yake, “Me na yi?” Kamar dokin da ya kutsa kai cikin fagen fama.


A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.


Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba.


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.”


Domin ka kawo mana abin da yake baƙo a gare mu, muna kuwa so mu san ma'anarsa.”


Ina tsoro kada in na sāke zuwa, Allahna ya ƙasƙanta ni a gabanku, in kuma yi baƙin ciki saboda waɗansu da yawa da suka yi zunubi a dā, ba su kuwa tuba da aikinsu na lalata ba, da fasikancinsu, da fajircinsu da suka aikata.


In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.


suka zagi Allah Mai Sama saboda azabarsu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.


Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala'i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.


Na ba ta damar tuba, amma ta ƙi tuba da fasikancinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan