Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin 'ya'yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”