Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:11 - Littafi Mai Tsarki

11 “Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:11
31 Iomraidhean Croise  

“Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuwa.


Ba wani abu tsarkakakke Da zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.


Akwai mutumin da yake tsarkakakke sarai? Akwai mutumin da yake cikakke a wurin Allah?


Akwai wanda ya isa ya zama adali, Ko mai tsarki a gaban Allah?


Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni, Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.


Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa'ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.


A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama'ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala'ikan Ubangiji a gabansu.


Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa, “ ‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.’


Tun daga zamanin Yahaya Maibaftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan riske shi.


A wannan zamani ne Yahaya Maibaftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya,


“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


Don haka duk wanda ya yar da umarni ɗaya mafi ƙanƙanta daga cikin umarnan nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a Mulkin Sama. Duk wanda ya bi su kuwa, har ya koyar da su, za a ce da shi mai girma a Mulkin Sama.


Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji, Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki Tun yana cikin uwa tasa.


“Ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka wanda ya fi ƙasƙanta a Mulkin Allah ya fi shi.”


Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”


Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”


shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”


mutane kuwa da yawa suka zo wurinsa, sai suka riƙa cewa, “Hakika, Yahaya bai yi wata mu'ujiza ba, amma duk abin da ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”


Shi kam, lalle ne ya riƙa ƙaruwa, ni kuwa in riƙa raguwa.


Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.


To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.


Don ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa Ikkilisiyar Allah.


In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikkilisiya?


Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara.


tun da Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau, sai kuwa tare da mu ne za a kammala su.


Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto,


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan