Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa, “ ‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:10
10 Iomraidhean Croise  

Murya tana kira tana cewa, “Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji! Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!


A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”


“Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.


“Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.


su ce masa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”


Wannan shi ne wanda Annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, “Muryar mai kira a jeji yana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji tafarki, Ku miƙe hanyoyinsa.’ ”


Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa, “Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya.


Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki, Gama za ka riga Ubangiji gaba, Domin ka shisshirya hanyoyinsa,


Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan