Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 11:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 11:1
19 Iomraidhean Croise  

kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa,


Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


Haka fa, suka fita, suna wa'azi mutane su tuba.


Sai suka fara matsa masa lamba, suna cewa, “Yana ta da hankalin jama'a, yana koyarwa a dukan ƙasar Yahudiya, tun daga ƙasar Galili har zuwa nan.”


Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,


In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.


Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku.


har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa'azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.


domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu.


Ai, ko dā ma, sa'ad da muke a tare, mun yi muku wannan umarni, cewa duk wanda ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.


To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu.


ka bi umarninsa, ba tare da wani aibi ko zargi ba, har ya zuwa bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan