9 Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,
9 “Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,
Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.
Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.
Ya kuma ce musu, “Sa'ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.”