Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:8
15 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan! Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome ba!


Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”


Sai ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da baƙaƙen aljannu, su warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’


Kada ku riƙi kuɗin zinariya, ko na azurfa, ko na tagulla a ɗamararku,


za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan, za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”


Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’


Amma Bitrus ya ce, “Kuɗi kam, ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. Da sunan Yesu Almasihu Banazare, yi tafiya.”


kana kuma miƙo hannunka kana warkarwa, ana kuma yin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi albarkacin sunan Baranka mai tsarki Yesu.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan