Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:7 - Littafi Mai Tsarki

7 kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, ‘Mulkin Sama ya kusato.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:7
19 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljannu. Kyauta kuka samu, ku kuma bayar kyauta.


Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.


To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah.


“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.


“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kun toshe wa mutane ƙofar Mulkin Sama. Ku kanku ba ku shiga ba, kuna kuwa hana masu niyyar shiga shiga.


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Tun daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, “Ku tuba domin Mulkin Sama ya kusato.”


Haka fa, suka fita, suna wa'azi mutane su tuba.


“Attaura da litattafan annabawa suna nan har ya zuwa ga Yahaya, daga lokacin nan kuwa ake yin bisharar Mulkin Allah, kowa kuma yana kutsawa zuwa ciki.


ya kuma aike su su yi wa'azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.


Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko'ina.


Sai Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu. Amma kai kuwa, tafi ka sanar da Mulkin Allah.”


Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dad dare, ya ce masa, “Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu'ujizan da kake yi, sai ko Allah yana tare da shi.”


Bitrus na shiga gidan ke nan sai Karniliyas ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada.


yana ta wa'azin Mulkin Allah, da koyar da al'amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.


don suna koya wa jama'a, suna tabbatar da tashi daga matattu, suna misali da Yesu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan