“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.
“Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu.
“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.
Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.
Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Hakika da yake tumakina sun zama ganimar dukan namomin jeji, saboda rashin makiyayin kirki, makiyayana kuma ba su nemo su ba, amma suka yi kiwon kansu, ba su yi kiwon tumakin ba,
Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.
Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.