Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:42 - Littafi Mai Tsarki

42 Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

42 In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:42
21 Iomraidhean Croise  

Ta juya ta tafi don ta kawo masa ruwan sha ke nan, sai ya sāke kiranta, ya ce, “Ki kuma kawo mini ɗan abinci.”


Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa'ad da ya zo ya sauka a wurin.”


Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.


haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.


Ka jefa kyautarka a baya, ka tsince ta a gaba.


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.


Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”


Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’


Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.


Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama 'ya'yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.


Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan