38 Wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai cancanci zama nawa ba.
38 duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.
Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.
Yesu ya dube shi duban ƙauna, ya ce masa, “Abu guda ne kawai ya rage maka. Sai ka je, ka sayar da duk mallakarka, ka ba gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”
Ya kira taron tare da almajiransa, ya ce musu, “Duk mai son bina, sai yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.
Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.
Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota.