Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:33
11 Iomraidhean Croise  

wato musun Ubangiji, da ƙin bin Allah, da maganar zalunci, da ta tayarwa, da shirya ƙarairayi a zuciya, da kuma hurta su.


Sai Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.”


Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.


Duk wanda zai ji kunyar shaida ni da maganata a wannan zamani na rashin amana da yawan zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi, sa'ad da ya zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'iku tsarkaka.”


Wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musun saninsa a gaban mala'ikun Allah.


Amma ya musa ya ce, “Ke, ban ma san shi ba.”


Duk wanda sai ya ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa'ad da ya zo da ɗaukaka tasa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala'iku tsarkaka.


In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi, In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,


Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.


Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan