31 Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.”
31 Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
Duk da haka in banda kai ba wanda ya fi shi, Ka naɗa shi da daraja da girma!
Ku dubi dai tsuntsaye. Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba sa kuma tarawa a rumbuna, amma kuwa Ubanku na Sama na ci da su. Ashe, ko ba ku fi martaba nesa ba?
Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!”