Mattiyu 10:30 - Littafi Mai Tsarki30 Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202030 Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. Faic an caibideil |
Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.