Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:28
30 Iomraidhean Croise  

Amma su yi tsoron Ubangiji Allahnsu, shi kuwa zai cece su daga hannun dukan abokan gābansu.


Saboda haka mutane suke tsoronsa, Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”


Saboda kai, nake jin tsoro, Na cika da tsoro saboda shari'unka.


Yawan mafarkanka, da dukan ayyukanka, da yawan maganganunka duk banza ne, duk da haka ya fi maka amfani ka yi tsoron Allah.


Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?


“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.


Ni kaina na halicci dukan kome ka kome! Ina jin daɗin waɗanda suke da tawali'u, da kuma masu tuba, waɗanda suke tsorona suna kuwa biyayya gare ni.


Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.


“Don haka kada ku ji tsoronsu, domin ba abin da yake a rufe da ba zai tonu ba, ko kuwa abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta su tashi, tashin rai, waɗanda suka yi rashin gaskiya kuwa su tashi, tashin hukunci.


Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”


Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.


Aka mayar wa mata da matattunsa da aka tasar. Waɗansu mutane kuma an azabta su har suka mutu, amma sun ƙi yarda da irin 'yancin da za a ba su, domin a tashe su su rayu da rayuwa mafi kyau.


Mai ba da Shari'a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wane ne har da za ka ɗora wa ɗan'uwanka laifi?


Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da yake daidai, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu.


Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan