Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:27
16 Iomraidhean Croise  

Wannan shi ne jawabi a kan kwarin wahayi. Me yake faruwa? Me ya sa jama'ar birni duka suke biki a kan rufin gidaje?


Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.


Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan soraye


Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.


“Na faɗa muku duk wannan ne domin in kawar muku da sanadin tuntuɓe.


Sa'ad da kuwa Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku cikin dukan gaskiya, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai faɗa, zai kuma sanar da ku al'amuran da za su auku.


“Duk wannan na faɗa muku da misalai ne. Lokaci yana zuwa da ba zan ƙara faɗa muku kome da misalai ba, sai dai in ba ku labarin Uba a sarari.


Sai almajiransa suka ce, “Yauwa! Yanzu ne fa kake magana a sarari, ba da misali ba!


A kowace rana ya yi ta muhawwara a cikin majami'a da Yahudawa, da waɗansu masu ibada, da kuma waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.


“Ku tafi, ku tsaya a cikin Haikali, ku sanar da jama'a duk maganar wannan rai.”


ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”


Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan