Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ya isa wa almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira maigida Ba'alzabul, to, mutanen gidansa kuma fa?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ya isa wa ɗalibi yă zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida Be’elzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:25
13 Iomraidhean Croise  

Ahaziya ya faɗo daga tagar benensa a Samariya, ya kuwa ji ciwo ƙwarai. Sai ya aiki manzanni, ya ce musu, “Ku tafi, ku tambayi Ba'alzabul, gunkin Ekron, ko zan warke daga wannan ciwo.”


Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”


In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka su ne za su zama alƙalanku.


Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”


Suka ce masa, “Ma iya.” Sai Yesu ya ce musu, “Ƙoƙon da ni zan sha, da shi za ku sha, baftismar da za a yi mini kuwa, da ita za a yi muku.


Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”


Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”


In kuma Shaiɗan ya rabu a kan gāba, yaya mulkinsa zai ɗore? Ga shi, kun ce da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu.


In kuwa da ikon Ba'alzabul nake fitar da aljannu, to, 'ya'yanku fa, da ikon wa suke fitarwa? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.


Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”


Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?”


Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.”


Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan