Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra'ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”
Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.