Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:2 - Littafi Mai Tsarki

2 To, ga sunayen manzannin nan goma sha biyu. Da fari, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, da Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:2
44 Iomraidhean Croise  

Bayan kwana shida sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da ɗan'uwansa Yahaya, ya kai su a kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.


Sa'an nan uwar 'ya'yan Zabadi ta matso wurinsa tare da 'ya'yanta, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi wani abu.


Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.


Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.


Da ya ci gaba sai ya ga waɗansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu ɗan Zabadi, da ɗan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da ubansu Zabadi, suna gyaran tarunansu. Sai ya kira su.


Da fitarsu daga majami'a, sai suka shiga gidan su Bitrus da Andarawas, tare da Yakubu da Yahaya.


Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake kallon Haikalin sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce.


Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar.


Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’


Da lokaci ya yi, sai ya zauna cin abinci, manzanninsa kuma suna tare da shi.


Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce musu, “Ku je ku shirya mana Jibin Ƙetarewa mu ci.”


haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”


Da manzanni suka dawo, suka gaya wa Yesu abin da suka yi. Sai ya tafi da su a keɓe zuwa wani gari wai shi Betsaida.


Sai Filibus ya je ya gaya wa Andarawas, Andarawas kuma ya zo da Filibus, suka gaya wa Yesu.


Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.


Sai ta yiwo gudu wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.”


Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare,


Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?”


Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan al'amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaida tasa tabbatacciya ce.


Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “Ku ma kuna so ku tafi ne?”


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba ni na zaɓe ku, ku goma sha biyu ba? To, ɗayanku Iblis ne.”


Wato, yana nufin Yahuza, ɗan Saminu Iskariyoti, don shi ne zai bāshe shi, ko da yake ɗaya daga cikin goma sha biyun nan ne.


Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,


Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.


Sai suka yi musu kuri'a, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi a cikin manzannin nan goma sha ɗaya.


har ma ya sare Yakubu ɗan'uwan Yahaya da takobi.


To, Bitrus da Yahaya suna tafiya Haikali a lokacin addu'a, da ƙarfe uku na yamma,


Sa'an nan ya bayyana ga Yakubu, sa'an nan ga dukan manzanni.


Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,


Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,


Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,


Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya,


Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.


Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,


Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.


Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama! Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”


Ni Yahaya, ni ne na ji, na kuma ga waɗannan abubuwa. Sa'ad da kuwa na ji su, na kuma gan su, sai na fāɗi a gaban mala'ikan da ya nuna mini su, domin in yi masa sujada.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan