Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:18
15 Iomraidhean Croise  

Zan hurta umarnanka ga sarakuna, Ba kuwa zan ji kunya ba.


Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu.


A lokacin da suka ba da ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku faɗa, domin za a ba ku abin da za ku faɗa a lokacin.


Sai Yesu ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka gaya wa kowa kome. Sai dai ka je wurin firist ya gan ka, ka kuma yi sadaka domin tabbatarwa a gare su, kamar yadda Musa ya umarta.”


“Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.


Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,


Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.


Bayan da suka ƙare shaidarsu, sai wata dabba mai fitowa daga mahallaka tă yaƙe su, ta cinye su, ta kashe su,


Da ya ɓamɓare hatimi na biyar, na ga rayukan waɗanda aka kashe saboda Maganar Allah, da shaidar da suka yi a ƙarƙashin bagadin ƙona turare.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan