Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:17
26 Iomraidhean Croise  

Kada ka dogara ga maƙwabcinka, Kada kuma ka amince da abokinka. Ka kuma kame bakinka daga matarka Wadda take kwance tare da kai.


Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma.


su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”


Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.


To, sai manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi.


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


Ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa a kashe shi, uba kuwa ɗansa. 'Ya'ya kuma za su tayar wa iyayensu har su sa a kashe su.


“Amma ku kula da kanku, don za su kai ku gaban majalisa, a kuma yi muku dūka a majami'u. Za a kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda sunana, domin ku ba da shaida a gabansu.


Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,


Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka?


Za su fisshe ku daga jama'a. Hakika, lokaci ma na zuwa da kowa ya kashe ku, zai zaci bautar Allah yake yi.


Nan da nan kuwa 'yan'uwa suka tura Bulus bakin bahar, amma Sila da Timoti suka dakata a nan.


Ni kuma na ce, ‘Ya Ubangiji, ai, su ma kansu sun sani a kowace majami'a na ɗaɗɗaure waɗanda suka gaskata da kai, na kuma daddoke su.


Na kuma sha gwada musu azaba a dukan majami'u, ina ƙoƙarin sa su yin saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.”


ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.


Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma'aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan!


Kai ma, ka mai da hankali da shi, gama ya hauri maganarmu, mummunan hauri.


Har wa yau kuma, waɗansu suka sha ba'a da bulala, har ma da ɗauri da jefawa a cikin kurkuku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan