Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 10:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Kowa kuma ya ƙi yin na'am da ku, ko kuwa ya ƙi sauraron maganarku, da fitarku gidan ko garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 10:14
14 Iomraidhean Croise  

Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.” Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.


In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku.


“Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa.


Duk inda aka ƙi yin na'am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunka don shaida a kansu.”


“Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”


Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”


Duk waɗanda ba su yi na'am da ku ba, in za ku bar garin, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”


Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”


Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya.


Da suka mūsa masa, suna ta zaginsa, ya karkaɗe tufafinsa ya ce musu, “Alhakinku yana a wuyanku! Ni kam na fita. Daga yau wurin al'ummai zan je.”


Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan