12 In za ku shiga gidan ku ce, ‘Salama alaiku.’
12 Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.
Salama ta samu a garukanki, Da zaman lafiya kuma a fādodinki.”
Saboda abokaina da aminaina, Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”
Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.
Duk gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma baƙunce shi har ku tashi.
In gidan na kirki ne, salamarku tă tabbata a gare shi. In kuwa ba na kirki ba ne, to, tă komo muku.
Allah ya aiko wa Isra'ilawa maganarsa, ana yi musu bisharar salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.
Saboda haka, mu jakadu ne na Almasihu, wato, Allah na neman mutane ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Almasihu, ku sulhuntu da Allah.
Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.
Gaisuwar da za ku yi masa ke nan, ku ce, ‘Salama gare ka, salama ga gidanka, salama kuma ga dukan abin da kake da shi.