Ta haka sarki Azariya ya kuturce, har zuwa ranar mutuwarsa. Saboda kuturtarsa, ya zauna a keɓe a wani gida, gama an fisshe shi daga Haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa shi ya shugabanci iyalin gidan sarki, yana kuma mulkin jama'ar ƙasa.
Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Yerusha 'yar Zadok.