Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Yesse ya haifi sarki Dawuda. Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:6
25 Iomraidhean Croise  

Sai ya aika a bincika ko wace ce wannan mata, ashe, 'yar Ammiyel ce, matar Uriya Bahitte.


Wannan ita ce maganar Dawuda ta ƙarshe. Dawuda ɗan Yesse, shi ne mutumin da Allah ya ɗaukaka, wanda Allah na Yakubu ya zaɓa ya zama sarki, wanda kuma ya shirya waƙoƙin Isra'ila. Dawuda ya ce,


domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.


Ga sunayen 'ya'yan da aka haifa masa a Urushalima, Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu,


da Ozem, da Dawuda. Su 'ya'ya maza bakwai ke nan.


Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.


Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.


Ƙarshen addu'o'in Dawuda, ɗan Yesse ke nan.


Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.


Salmon ya haifi Bo'aza (uwa tasa Rahab ce), Bo'aza ya haifi Obida (mahaifiyarsa Rut ce), Obida ya haifi Yesse,


Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.


Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”


Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.


Saul ya tambayi Dawuda, ya ce, “Saurayi, kai ɗan wane ne?” Dawuda ya amsa, ya ce, “Ni ɗan baranka ne, Yesse, mutumin Baitalami.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan