Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:23 - Littafi Mai Tsarki

23 “Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, Za a kuma sa masa suna Immanuwel.” (Ma'anar Immanuwel kuwa itace Allah na tare da mu.)

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:23
18 Iomraidhean Croise  

Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!


Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!


Allah ne Mai Cetona, Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba. Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi, Shi ne Mai Cetona.”


Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.


Da Yusufu ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala'ikan Ubangiji, ya ɗauki matarsa,


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Dawuda ya ce shi Ubangiji ne. To, ƙaƙa zai zama ɗansa?”


Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


Wata rana da daddare, Ubangiji ya yi wa Bulus wahayi, ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, sai dai ka yi ta wa'azi, kada ka yi shiru,


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.


wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta 'yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa.


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.


Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan