Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:20
38 Iomraidhean Croise  

Sai mala'ikan Allah ya ce mini a cikin mafarki, ‘Yakubu,’ sai na ce, ‘Ga ni.’


Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma.


Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini 'yar waina, ki kawo mini, sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki.


Ubangiji kuwa ya bayyana ga Sulemanu cikin mafarki a Gibeyon da dare, ya ce masa, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”


Ni bawanka ne, don haka ka ba ni ganewa, Don in san koyarwarka.


A gare ka nake dogara, Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka. Addu'ata ta hau zuwa gare ka, Ka nuna mini hanyar da zan bi.


Sa'ad da nake alhini, ina cikin damuwa, Ka ta'azantar da ni, ka sa in yi murna.


Amintattun mutane za su yi maka abin da yake daidai, amma mugaye za su ruɗe ka.


Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji, Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi, Waɗanda suke dogara gare ka.


Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”


“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.


Ga amsar da Ishaya ya ba Ahaz, “Kasa kunne yanzu, kai zuriyar sarki Dawuda. Ba abin kirki kuke yi ba, da kuka ƙure haƙurin jama'a, haƙurin Allah kuma kuke so ku ƙure?


Labari ya kai gun Sarkin Yahuza, cewa sojojin Suriya sun shiga ƙasar Isra'ila. Sai shi da dukan jama'arsa suka firgita ƙwarai, suna ta kaɗuwa kamar itatuwan da iska take kaɗawa.


Har yaushe za ki yi ta shakka, Ya ke 'yar marar bangaskiya? Gama Ubangiji ya halitta sabon abu a duniya, Mace ce za ta kāre namiji.”


sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”


Gedaliya ɗan Ahikam, jikan shafan ya rantse musu da mutanensu, ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Kaldiyawa, ku yi zamanku a ƙasar, ku bauta wa Sarkin Babila, za ku kuwa zauna lafiya.


“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.


Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.


Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.


Amma da aka gargaɗe su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.


Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”


Amma bayan mutuwar Hirudus, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar, ya ce,


Amma da ya ji Arkilayus ya gāji ubansa Hirudus, yana mulkin ƙasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Amma da aka yi masa gargaɗi a mafarki, sai ya ratse zuwa ƙasar Galili.


Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.”


Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.


Sai mala'ikan ya amsa ya ce, “Ni ne Jibra'ilu da yake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir.


Yusufu shi ma ya tashi daga birnin Nazarat, a ƙasar Galili, ya tafi ƙasar Yahudiya, ya je birnin Dawuda, da ake kira Baitalami (domin shi daga gidan Dawuda ne, na cikin zuriyarsa),


Amma da daddare sai wani mala'ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce,


Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa, Mu kuma ɗaukaka shi, Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo, Amaryarsa kuma ta kintsa.


Ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan