Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Yusufu mijinta kuwa da yake shi mutumin kirki ne, ba ya kuma so ya ba ta kunya a gaban jama'a, sai ya yi niyyar rabuwa da ita a asirce.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:19
15 Iomraidhean Croise  

Bayan misalin wata uku, aka faɗa wa Yahuza, “Tamar surukarka ta yi lalata, har ma tana da ciki.” Sai Yahuza ya ce, “A fito da ita, a ƙone ta.”


Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.


“Idan mutum ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda kuma wani yake tashinta, tun ba a fanshe ta ba, ko kuwa ba a 'yanta ta ba, sai a bincike, amma ba za a kashe su ba, domin ita ba 'yantacciya ba ce.


“Idan mutum ya yi zina, sai a kashe dukansu biyu, wato, shi da mazinaciyar.


Suka ce, “Musa ya ba da izini a rubuta takardar kisan aure, a kuma saki matar.”


don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.


To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.


Sai suka ce, “Wani jarumi ne, wai shi Karniliyas, mutumin kirki, mai tsoron Allah, wanda duk jama'ar Yahudawa suke yabo, shi ne wani tsattsarkan mala'ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.”


Da gari ya waye ba su shaida ƙasar ba, amma dai sun lura da wani lungu da gaci mai yashi, sai kuma suka yi shawara cewa in mai yiwuwa ne su kai jirgin kan yashin.


Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.


“Idan aka tabbatar zargin gaskiya ne, ba a kuma ga shaidar budurcinta ba,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan