Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:16
17 Iomraidhean Croise  

Aliyudu ya haifi Ele'azara, Ele'azara ya haifi Matana, Matana ya haifi Yakubu,


Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.”


Sai ya kwaɓi almajiransa ƙwarai kada su gaya wa kowa shi ne Almasihu.


Da suka tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, “Tashi ka ɗauki ɗan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu ƙasar Masar, ka zauna a can sai na faɗa maka, don Hirudus yana shirin binciko ɗan yaron yă hallaka shi.”


Da suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sakar muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake kira Almasihu?”


Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!”


Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.


gun wata budurwa da aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu, na zuriyar Dawuda, sunan budurwar kuwa Maryamu.


Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”


Sai ta haifi ɗanta na fari, ta rufi shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komi dabbobi, don ba su sami ɗaki a masaukin ba.


Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli,


Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”


Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan