Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 1:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Bayan an ɗebe su zuwa Babila, sai Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Shayeltiyel ya haifi Zarubabel,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon. Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 1:12
20 Iomraidhean Croise  

Nebukadnezzar ya kwashe dukan mutanen Urushalima, da dukan hakimai da dukan jarumawa, da masu sana'a, da maƙera, har sun kai dubu goma (10,000). Ba wanda ya ragu sai dai matalautan ƙasar.


A rana ta ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu, a shekara ta talatin da bakwai ta ɗaurin Yekoniya Sarkin Yahuda, sai Ewil-merodak da ya zama Sarkin Babila ya yi wa Yekoniya alheri, ya sake shi a shekarar da ya ci sarautar.


'Ya'yan Yekoniya wanda aka kama, su ne Sheyaltiyel,


Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da 'yan'uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da 'yan'uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra'ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.


Sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozodak, suka tashi suka sāke kama aikin gina Haikalin Allah wanda yake a Urushalima. Annabawan Allah suna tare da su, suna taimakonsu.


Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su ne Seraiya, da Irmiya, da Ezra,


“Ni Ubangiji na rantse da raina, ko da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, zoben hatimi ne a yatsan hannun damana, duk da haka zan kwaɓe shi,


Ashe, Yekoniya kamar fasasshen tulu yake, Wanda ba wanda ya kula da shi? Me ya sa aka watsar da shi da 'ya'yansa, A ƙasar da ba su sani ba?


Haka Ubangiji ya ce, “Rubuta wannan mutum, marar 'ya'ya. Mutumin da ba zai yi albarka a duk kwanakinsa ba. Gama ba wani daga zuriyarsa Da zai gāji gadon sarautar Dawuda, Ko ya yi mulki kuma a Yahuza.”


wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.


A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.


Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.


Ubangiji kuwa ya zuga zuciyar Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da zuciyar dukan sauran mutane. Suka zo, suka fara aikin Haikalin Ubangiji Allahnsu Mai Runduna


“Ka yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, ka ce,


A wannan rana, ni Ubangiji Mai Runduna, zan ɗauke ka, kai Zarubabel, bawana ɗan Sheyaltiyel, in maishe ka kamar zobe mai hatimi, gama na zaɓe ka, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’ ”


Yosiya ya haifi Yekoniya da 'yan'uwansa, wato, a lokacin da aka ɗebe su zuwa Babila.


Zarubabel ya haifi Abihudu, Abihudu ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azuro,


Wato, dukkan zuriya daga Ibrahim zuwa kan Dawuda, zuriya goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa ga ɗebe su a kai Babila kuwa, zuriya goma sha huɗu. Daga ɗebe su zuwa Babila zuwa kan Almasihu, zuriya goma sha huɗu.


Yahuza ɗan Yowana, Yowana ɗan Refaya, Refaya ɗan Zarubabel, Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ɗan Niri,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan