Bisa ga umarnin Ubangiji, sai annabin ya ta da murya, ya ce, “Ya bagade, bagade, Ubangiji ya ce za a haifi ɗa a gidan Dawuda, sunansa Yosiya wanda zai miƙa firistoci na masujadan tuddai hadaya a kanka, wato firistoci waɗanda suke ƙona turare. Za a ƙone ƙasusuwan mutane a bisa kanka.”
Sai Hezekiya ya rasu, suka binne shi a sashe na bisa na hurumin 'ya'yan Dawuda, maza. Dukan Yahuza da mazaunan Urushalima suka girmama shi sa'ad da ya rasu. Sai Manassa ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.