Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 5:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Mun miƙa hannu ga Masar da Assuriya Don mu sami abinci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 5:6
15 Iomraidhean Croise  

Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,


Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.


Kun tafi wurin Molek da mai, da turare iri iri da kuka riɓaɓɓanya. Kun aika jakadunku can nesa, kun aike su su gangara, har zuwa lahira.


Wace riba ka samu, har da ka tafi Masar, Don ka sha ruwan Kogin Nilu? Wace riba ka samu, har da ka tafi Assuriya, Don ka sha ruwan Kogin Yufiretis?


Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya, Sai ku yi nan ku yi can? Masar za ta kunyata ku kamar yadda Assuriya ta yi.


Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi! Ta ba da gari, Ginshiƙanta sun fāɗi. An rushe garunta, Gama wannan sakayya ce ta Ubangiji. Ku sāka mata, ku yi mata kamar yadda ta yi.


Idanunmu sun gaji Da zuba ido a banza don samun taimako, Mun zuba ido Ga al'ummar da ba za ta iya cetonmu ba.


Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.


Ifraimu tana kiwon iska, Tana ta bin iskar gabas dukan yini. Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya. Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya, Tana kai mai a Masar.”


“Sa'ad da Ifraimu ta ga ciwonta, Yahuza kuma ta ga rauninta, Sai Ifraimu ta aika zuwa Assuriya, Wurin babban sarki. Amman ba zai iya warkar da ciwonki, ko rauninki ba.


Ifraimu kamar kurciya take, marar wayo, marar hankali, Takan tafi Masar da Assuriya neman taimako.


Ba za su zauna a ƙasar Ubangiji ba, Amma mutanen Ifraimu za su koma Masar. Za su ci haramtaccen abinci a Assuriya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan