Yanzu fa Ubangiji, Ubangiji Mai Runduna, yana gab da ya kwashe kowane abin da kowane mutum da jama'ar Urushalima da na Yahuza suke dogara da su. Zai kwashe abincinsu da ruwan shansu,
Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan! Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome ba!
domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.