“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.
Ya Urushalima, tsatsarki ita ce ƙazantar lalatarki. Da yake na tsabtace ki, ba ki tsabtatu ba, To, ba za ki ƙara yin tsabta ba, Har lokacin da na fashe fushina a kanki.’
Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’
Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi 'ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha'u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama'ar Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata.