Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 5:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ya Ubangiji, ka komo da mu zuwa gare ka! Mu kuwa za mu koma. Ka sabunta kwanakinmu su zama kamar na dā.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 5:21
19 Iomraidhean Croise  

Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, domin waɗannan mutane su sani, kai Ubangiji, kai ne Allah, kai ne kuma ka juyo da zuciyarsu.”


Ka komo da mu, ya Ubangiji Allah Mai Runduna! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!


Ka komo da mu, ya Allah! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!


Ka komo da mu, ya Allah Mai Runduna! Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!


Ka komo da mu, ya Allah Mai Cetonmu, Ka daina jin haushinmu!


Kwanakin baƙin cikinki za su ƙare. Ni, Ubangiji, zan zama madawwamin haskenki, Mai daɗewa fiye da na rana da na wata.


'Ya'yansu za su zama kamar dā, Jama'arsu kuma za su kahu a gabana, Zan hukunta dukan waɗanda suka zalunce su.


“Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana cewa, ‘Ka hore ni, na kuwa horu, Kamar ɗan maraƙin da ba shi da horo, Ka komo da ni don in zama kamar yadda nake a dā, Gama kai ne Ubangiji Allahna.


Haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan wuri da ka ce ya zama kufai, ba mutum ko dabba, wato a biranen Yahuza da titunan Urushalima, inda ba kowa, ba mutum ko dabba a ciki,


A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.


Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki.


Ya Ubangiji, na ji labarinka, Sai tsoro ya kama ni. Ka maimaita manyan ayyukanka a zamaninmu, Ayyukan da ka saba yi. Ka yi jinƙai ko lokacin da kake fushi.


Sa'an nan kuma Ubangiji zai yarda da hadayun mutanen Yahuza da na Urushalima kamar yadda yake a zamanin dā.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan