Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”
Gama sun shuka iska Don haka zu su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya, Ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,
Za a washe dukiyarsu, Za a kuwa rurrushe gidajensu, Ko da yake sun gina gidaje, ba za su zauna a ciki ba, Ko da yake sun dasa inabi, ba za su sha ruwansa ba.”