Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Makoki 5:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Amma ya Ubangiji, kai ne kake mulki har abada, Kursiyinka ya dawwama har dukan zamanai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Makoki 5:19
23 Iomraidhean Croise  

Ubangiji sarki ne har abada abadin, Arna kuma za su ɓace daga ƙasarsa.


Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada, Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.


Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne kai har abada.


Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamanai! Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!


Ubangiji yana sarautar ruwa mai zurfi, Yana sarauta kamar sarki har abada.


Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin! Kana mulkin mallakarka da adalci.


Amma Ubangiji sarki ne har abada, Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.


Kafin a kafa tuddai, Kafin kuma ka sa duniya ta kasance, Kai Allah ne, Madawwami. Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.


Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko, Kana nan tun fil azal.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta, Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa. Mulkinsa, madawwamin mulki ne, Wanda ba zai ƙare ba. Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”


Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’


Ba kai ne madawwami ba? Ya Ubangiji Allahna Mai Tsarki. Ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji, kai ne ka sa su su yi hukunci, Ya dutse, kai ne ka kafa su don su yi horo.


Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”


Allah Madawwami, shi ne wurin zamanka, Madawwaman damatsansa suna tallafarka, Yana kore maka maƙiyanka, Ya ce, ‘Ka hallaka su!’


Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.


Yesu Almasihu ba ya sākewa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma.


Daga Yahaya zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai da suke a ƙasar Asiya. Alheri da salama su tabbata a gare ku daga wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da suke a gaban kursiyinsa,


“Ni ne Alfa. Ni ne Omega,” in ji Ubangiji Allah, wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, Maɗaukaki.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan